OPEC

Kasashen OPEC na gudanar da taro dan rage yawan man da su ke hakowa

Taron ministocin kasashen kungiyar OPEC
Taron ministocin kasashen kungiyar OPEC REUTERS/Waleed Ali

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC da mukarrabanta za su gudanar da taro ta kafar bidiyo a ranakun Litinin da Talata don tattaunawa a kan rage yawan danyen man da kasashen da ke cikinta ke samarwa, yayin da annobar Coronavirus ke ci gaba da rage bukatar danyen mai a duniya.

Talla

Taron na zuwa ne a yayin da bangaren man fetur ke fatar murmurewa daga mummunar tasirin annobar da ta tilasta wa kungiyar OPEC rage yawan danyen man da take samarwa sakamakon raguwar da aka samu na bukatar sa a duniya saboda bullar annobar Covid 19.

Kasashen da ke cikin wannan kungiyar dai na kokarin yin duk mai yiwuwa ne wajen ganin ba a samu matsalar faduwar darajar gangar danyen mai kamar yadda aka samu a watan Afrilu ba.

Bisa yarjejeniyar da aka cimma a watan Afrilun, ana sa ran sake rage ganga miliyan 7 da dubu dari 7 na danyen mai da ake samarwa kowace rana zuwa miliyan 5 da dubu dari 8 duk rana a watan Janairun 2021, amma akasarin masu lura da al’amura na ganin za a yi tsawaitawa da watanni 3 zuwa 6.

Masu kumban susa a cikin wannan kungiya ta OPEC sun tsegunta a ‘yan makonnin da suka wuce cewa akwai yiwuwar duba batun rage danyen man da ake samarwa, duk da labari mai karfafa gwiwa na nasarar da wasu kamfanoni suka samu ta lalubo allurar rigakafin Coronavirus.

A yayin da ake ganin kungiyar na iya ci gaba da rage yawan danyen man da take samarwa, akwai kuma yiwuwar samun gutsiri tsoma a tsakanin kasashe 23 da ke cikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.