Wasanni

Messi ya girmama Maradona

Diego Maradona da Lionel Messi
Diego Maradona da Lionel Messi REUTERS/Enrique Marcarian

Lionel Messi ya jinjina wa marigayi Diego Maradona bayan da ya ci kwallo a karawar da Barcelona ta doke Osasuna da 4-0 a gasar La Liga da suka fafata ranar Lahadi.

Talla

Dan wasan gaban da yanzu haka ke amatsyin gwarzon kwallon kafar kasar Agentina da ma duniya, mai shekara 33, bayan cin kwallon ya daga rigarsa, inda aka ga jesin Newell ta Old Boys – wato daya daga cikin tsofaffin kungiyoyin Argentina da Maradona ya taka leda ya bayyana a karkashin rigar tasa.

Kafin kuma ya daga kai ya hangi manyan akwatunan talabijin dake nuna hoton Maradona da ya kewaye filin wasan na Camp Nou tare da daga hannayensa biyu sama, wato allamar girmamawa ga tsohon gwarzon kasar Maradona.

Martin Braithwwaite, da Antoine Griezmann da Philippe Coutinho duk sun ci kwallo a wasan na jiya.

Maradona, wanda ke daya daga cikin fitattun 'yan wasan lokacin sa, ya mutu a ranar Laraba yana da shekara 60.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.