WHO-Coronavirus

WHO ta sha alwashin gano nau'in dabbar da ta yada Covid-19

Zuwa yanzu cutar ta kashe mutane miliyan guda da dubu 460 a fadin Duniya.
Zuwa yanzu cutar ta kashe mutane miliyan guda da dubu 460 a fadin Duniya. 路透社图片

Hukumar Lafiya ta Duniya ta sha alwashin gano dabbar da ke haifar da cutar korona, inda ta ke cewa matakin ya zama wajibi domin kare aukuwar haka a nan gaba.

Talla

Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus ya bayyana haka, inda ya ke cewa gano assalin cutar na da muhimmanci ga Hukumar, yayin da ya bukaci masu bukatar tuhumar kasar China inda aka fara samun barkewar cutar da su daina.

Kasar Amurka da ta yi asarar rayukan mutane sama da 262,000 tayi mummunar suka ga Hukumar saboda yadda ta tinkari matsalar da kuma yadda ta rufawa Chinar asiri dangane da annobar da ta samo assail daga Wuhan.

Wasu masu sukar sun kuma zargi Hukumar Lafiyar da baiwa China damar jan akalar ayyukan ta da suka shafi bincike kan cutar, wanda ya kaiga shugaba Donald Trump katse kudaden da Amurka ke baiwa Hukumar.

Ya zuwa yanzu cutar ta kashe mutane miliyan guda da dubu 460 a fadin duniya, bayan ta harbi mutane sama da miliyan 63.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.