Lafiya

Covid-19 ta haddasa koma-baya a yaki da Kanjamau

Kimanin mutane miliyan 38 ke rayuwa tare da cutar Kanjamau a sassan duniya.
Kimanin mutane miliyan 38 ke rayuwa tare da cutar Kanjamau a sassan duniya. REUTERS/Rupak De Chowdhuri

Yau 1 ga watan Disamba, rana ce da Majaliar Dinkin Duniya ta ware domin tunawa da cutar Kanjamau wadda ke ci gaba da barna duk da ci gaban da aka samu wajen yaki da cutar. Annobar coronavirus ta kara haddasa fargabar tsanantar cutar ta Kanjamau a duniya.

Talla

A bara kadai, mutane miliyan 1 da dubu 700 suka kamu da cutar Kanjamu, yayin da miliyan 38 ke rayuwa tare da cutar a sassan duniya.

Masu fama da wannan cuta za su iya rayuwa amma da sharadin samun kaluwa, sannan kuma ba sa barazanar yada cutar.

Akwai bukatar jama’a su san halin da suke ciki game da cutar ta Kanjamau, sannan a samar musu da kyakkyawan yanayin shan magunguna musamman tsakanin mutanen da suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar da suka hada da ‘yan luwadi da ‘yan kwaya da fursunoji da kuma karuwai.

Mutanen da ake tsangwama saboda Kanjamu, na rasa damar samun magunguna a mafi tarin lokuta, sannan kuma suna dauke da kashi 60 cikin 100 na yada wannan cuta.

Babbar matsalar da ake fuskanta ita ce, jinkirin gano masu dauke da cutar ta HIV da kuma samun damar shan magunguna.

Alkaluma sun nuna cewa, ana yi wa mutun takwas cikin goma gwajin cutar, inda bakwai daga cikin goma ke samun magunguna , yayin da shida daga cikin goma ke shawo kan cutar.

Wadannan alkaluma sun yi karanci, muddin ana muradin kawo karshen cutar ta Kaanjamau baki daya nan da shekara ta 2030 kamar yadda kashen duniya ke buri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.