Majalisar Dinkin Duniya

Mutane miliyan 235 ne za su bukaci agajin gaggawa a 2021- MDD

Sakatare Jnar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Jnar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Lisi Niesner

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane miliyan 235 za su bukaci taimakon agajin gaggawa a shekarar 2021, kuma miliyan 160 daga cikin su za su samu kan su cikin mummunar yanayin da za a bukaci akalla Dala biliyan 35 domin samar musu da kayan jinkai.

Talla

Rahotan da Sakatare Janar na Majalisar Antonio Guterres da wasu hukumomi da kungiyoyin da ke aiki tare da su suka gabatar, ya ce matsalar za ta shafi kasashen duniya 56 sakamakon tashe-tashen hankula da kuma annobar korona.

Guterres ya ce ganin yadda adadin mutanen da ke bukatar taimakon ya karu da kusan kashi 40 sabanin na shekarar 2020, ya zama wajibi manyan kasashen duniya su taimakawa wadannan mutane wadanda ke fuskantar mummunan yanayi.

Sakataren ya ce inda za a tattara wadannan mabukata miliyan 235 a cikin kasa guda, zata kasance kasa ta 5 mafi yawan mutane a duniya.

Shugaban Hukumar Jinkai ta Majalisar Dinkin Dunkiya Mark Lowcork ya ce ganin yadda manyan kasashen duniya suka fara murmurewa daga annobar korona, abin ba haka ya ke a kasashe matalauta ba, lura da yadda cutar ta jefa miliyoyin mutane zuwa cikin tsananin talauci.

Lowcock ya bukaci duniya ta sauya yadda ta ke tafiya wajen rage yawan irin mutanen da ke bukatar agajin gaggawa da kuma dakile cutar korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.