Amurka-Trump

Trump na yunkurin karshe na dakile tasirin baki a majalisar wakilai

Donald Trump na Amurka.
Donald Trump na Amurka. (AP / JPP)

Gwamnatin shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump, ta kaddamar da yunkurinta na karshe a gaban kotun koli na neman a ware bakin hauren da ba su da rajistar daga cikin mutanen da ake amfani da su wajen tantance wakilan jihohi.

Talla

Idan har shirin na shugaban Amurka mai barin gado ya yi nasara, jihohin da ke da dimbim bakin hauren da ba su da rajista za su rage tasiri a majalisar wakilan Amurka.

Hakan zai kasance tamkar nasara a dakikokin karshe ga Trump, wanda ke daf da barin fadar White House tare da mika mulki ga zababben shugaban Amurka Joe Biden a ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2021, duk da cewa yana ci gaba da kin amincewa da shan kaye.

Kundin tsarin mulkin Amurka dai ya tanadi a gudanar da kidayar jama’a duk bayan shekaru 10, wanda sakamakon ake tantancve irin ayyukan da ake rangada wa al’umma da kuma yawan kujerun da kowace jiha ke samu a majalisar wakilan kasar.

Trump, dan jam’iyyar Republican, wanda ya shafe ilahirin wa’adin shugabancinsa yana kokarin rage kwararar bakin haure ya ce baya kaunar barin bakin haure su samu wakilci a majalisun kasar ba bisa ka’ida ba.

Har yanzu kidayar jama’a a Amurka ta hada ne da ilahirin mazauna jihohin kasar banda bakin da ke da bizar zama na wucin gadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.