Amurka

Gwamnatin Biden za ta yi ganawar gaggawa da Iran

Zababben shugaban  Amurka Joe Biden
Zababben shugaban Amurka Joe Biden AP Photo/Andrew Harnik

Shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden zai bukaci tattaunawar gaggawa da kasar Iran da zarar kasarsa ta koma cikin yarjejeniyar nukiliyar da ta fice a karkashin mulkin shugaba Donald Trump.

Talla

Biden ya shaida wa Jaridar New York Times cewar, batun na da tsauri, amma da zarar Iran ta koma mutunta yarjejeniyar da aka kulla, Amurka za ta koma cikin ta kafin fara tattaunawa.

Jaridar ta ce, gwamnatin Biden za ta kara wa’adin takaita tace sinadarin Uranium da Iran ke yi domin samar da makamin nukiliya.

Shugaban ya kuma ce ya zama wajibi Iran ta daina amfani da kawayenta wajen tada hankali a kasashen Lebanon da Iraqi da Syria da kuma Yemen tare da Saudi Arabia.

Yayin yakin neman zabensa, Biden ya yi alkawarin bai wa Iran kofar diflomasiyya domin mutunta yarjejeniyar da aka kulla da ita.

Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus da Rasha da Kungiyar Turai da kuma Majalisar Dinkin Duniya suka kulla yarjejeniyar nukiliyar Iran a shekarar 2015 wadda za ta hana ta mallakar makamin nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.