Abinci

Farashin abinci ya kai kololuwa wajen tsada a Duniya- FAO

Farashin kayan abinci dangin hatsi ya karu da kashi 20 akan yadda aka sayesu bara.
Farashin kayan abinci dangin hatsi ya karu da kashi 20 akan yadda aka sayesu bara. Zoé Berri

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce farashin abinci ya kai kololuwar tsada a bana a kusan dukkannin sassan duniya, fiye da yadda aka gani shekaru 6 da suka gabata.

Talla

Hukumar abincin ta FAO ta ce tashin farashin abinci dama karancinsa a sassan Duniya ya sanya fargaba da tashin hankali ga kasashe 45 da basa iya ciyar da al’ummarsu face sai da taimakon abinci daga ketare.

Hukumar wadda ke alakanta karuwar farashin kayakin abincin da mummunan yanayin da Duniya ta tsinci kanta, ta ce farashin yak ai kololuwa a watan Oktoban da ya gabata inda karuwar farashin ya tashi daga kashi 3.9 zuwa kashi 6.5.

Alkaluma a cewar rahoton ya nuna cewa karuwar farashin na wata-wata da hukumar ke bin diddigi ya yi tashin da rabon da Duniya ta fuskanci irinsa tun cikin watan Disamban shekarar 2014 ko da ya ke har aynzu bai kai irin tashin farashin kayakin abincin da aka gani a watan Yulin 2012 ba.

Rahoton hukumar ta FAO ya ce farashin man girki ne kan gaba a jerin kayakin abincin da suka kai kololuwa wajen tsada, wanda ya tashi da kashi 14.5 kana nau’ikan abinci dangin hatsi daya tashi da kashi da farashinsa ya karu da kashi 2.5 kwatankwacin karin kashi 20 na farashin da aka sayesu bara, kana suga da kashi 3.3.

Hukumar ta ce karuwar farashin na da nasaba da rage yawan kayakin noman da Argentina ta yi baya ga saye tarin kayakin masarufi da China ta yi da kuma halin da Duniya ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.