Isra'ila-Falasdinu

Isra'ila ta sakarwa Falasdinu kudadenta fiye da biliyan guda da ta rike

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. REUTERS/Abir Sultan/Pool

Isra’ila ta saki sama da Dala biliyan 1 daga cikin kudaden Falasdinu da ta rike, inda a yanzu ta aike wa hukumomin na Falasdinu wadannan makudan kudade bayan bangarorin biyu sun cimma wata sabuwar matsaya.

Talla

A wani sako da Firaministan falasdinu Mohammed Shtayyeh ya wallafa a Twitter wanda ke tabbatar da isar kudin asusun gwamnati ya ce tun farko hakkinsu ne da Isra'ilan ta karbe.

Matakin Isra'ilan wajen sakin kudaden Dala biliyan 1 da miliyan 15 na zuwa ne bayan wani rahoton bankin Duniya a baya-bayan nan da ke bayyana matsanancin halin da tattalin arzikin na yankin Falasdinu ke ciki.

Cikin rahoton na bankin Duniya, masana sun yi gargadin rugujewar tattalin arzikin yankin sakamakon koma bayan da ya samu saboda annobar covid-19 da ta kassara hada-hada.

Tun a watan mayun 2019, Isra’ila ke rike da kudaden na Falasdinu da yawansu ya haura Biliyan guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.