Coronavirus

Coronavirus ta kashe sama da mutane miliyan 1 da rabi

Wani dan yawon bude ido da ake wa gwajin cutar corona a Mexico.
Wani dan yawon bude ido da ake wa gwajin cutar corona a Mexico. REUTERS/Alexandre Meneghini

Annobar cutar corona da ta kama mutane miliyon 65 a fadin Duniya, ya zuwa yanzu, ta kashe sama da mutane miliyon daya da rabi, yayin da kasashe ke kokarin yin samar wa  al’ummominsu allurar rigakafi.

Talla

Ya zuwa wannan rana, cutar corona ta hallaka mutane miliyon daya da rabi yayin da a jimilce ta kama mutane sama da miliyon 65 a fadin Duniya, inji wani rahoton kamfanin dillacin labaran afp a Juma'a.

Alkalumma dai sun nuna cewa tun 24 ga watan nuwamban da ya gabata a kowace rana, mutane dubu goma cutar ke kashewa a dukan kasashen Duniya, sai ranar Alhamis inda mutane dubu 12658 suka kwanta dama, adadin da ba’a taba samun sama da shi ba na wadanda cutar ta kai lahira.

A wannan mako mutane dubu 601 da 700 ne suka mutu,  karin kashi 4 cikin 100.

Birtaniya da ta rasa 'yan kasarta dubu 60113, da ta animce tayi amfani da allurar rigakafin cutar da kamfanin Pfizer da BioNtech suka samar, ta ce ba za ta yi wa al’ummarta shaushawar ba muddin allurar rigakafin ta kasa cika ka’ida.

A yayin da a Faransa cutar ta lakume rayukan mutane dubu 54140, Amurka na sahun gaba da mamata dubu 276 da 401.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.