Bakonmu a Yau

Dr. Faskari kan walwalar addini a Najeriya

Sauti 03:51
Tamburan addinai
Tamburan addinai @ Godong/Universal Images Group via Getty Images

A karo na biyu Amurka ta sanya Najeriya a jerin kasashen da babu dama da walwalar gudanar da addini a cikinsu, a karkashin dokar kasa da kasa ta 1998 da ta bada wannan dama. Sai dai a wata sanarwa, gwamnatin Najeriya ta bakin ministan watsa labaranta, Lai Mohammed ta bayyana wannan mataki na Amurka a matsayin rashin fahimtar ummul’haba’isin rikice-rikice a kasar. A kan haka Michael Kuduson ya tattauna da Dr. Mainsara Umar Faskari, masanin shari’a da zamantakewa da dokokin kasa da kasa a Najeriya.