Sri Lanka

Mutumin da ya ce ya samu maganin corona ta hanyar wahayi

Har yanzu likitoci ba su tabbatar da maganin corona ba illa riga-kafinta.
Har yanzu likitoci ba su tabbatar da maganin corona ba illa riga-kafinta. Getty Images

Yanzu haka dubban 'yan kasar Sri Lanka ke tururuwa zuwa wani kauye domin karbar wani magani da wani kafinta ya ce Allah Ya ba shi ta hanyar mafarki, kuma yana warkar da cutar coronavirus.

Talla

Kafintan mai suna Dhammika Bandara ya bayyana haka ne ta kafar talabijin na kasa makon jiya, abin da ya sa jama’a daga birane ke ta tururuwa zuwa kauyen domin karbar maganin.

Sai dai likitoci a kasar sun ce, babu wata shaidar da ke tabbatar da sahihancin maganin, domin kuwa yanzu haka duniya ba ta samu maganin korona ba, sai dai na riga-kafi.

Rahotanni sun ce, hotan Ministan Lafiyar kasar, Pavithra Wanniarachchi da aka wallafa a jarida na kwankwadar maganin ya karfafa wa jama’a gwuiwar zuwa karbar sa.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya ce akalla mutane 12,000 suka yi tafiyar kilomita 85 daga birnin Colombo domin zuwa shan maganin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.