Coronavirus

Kasashe masu arziki na rige-rigen saye alluran rigakafin Korona

Wasu daga cikin alluran rigakafin cutar coronavirus da ake gaf da kammala gwajinsu.
Wasu daga cikin alluran rigakafin cutar coronavirus da ake gaf da kammala gwajinsu. Reuters

Gamayyar kungiyoyin fararen hula na kasa da kasa, sun yi gargadin cewa kasashe masu arziki na rige-rigen saye alluran rigakafin coronavirus tare da boye magungunan, abinda zai janyowa mutanen dake kasashe marasa karfi rasa damar samun rigakafin.

Talla

Gamayyar kungiyoyin dake kiran kansu da 'hadin gwiwar tabbatar da wadatar rigakafi ga dukkan mutane', sun yi gargadin cewa a halin da ake ciki, mutum daya cikin mutane 10 ne kawai zai iya samun allurar rigakafin cutar coronavirus a tsakanin kasashe matalauta kusan 70.

Wannan kalubale na zuwa ne duk da cewa hadin gwiwar jami’ar Oxford da kamfanin hada magunguna na AstraZaneca sun yi alkawarin samawa kasashen maso tasowa kashi 64 cikin dari na alluran rigakafin da suke bukata.

Alkaluman baya bayan nan dai sun nuna cewar jumillar kasashe masu arziki dake da kashi 14 na yawan al’ummar duniya tuni suka saye akalla kashi 53 na nau’ikan alluran rigakafin coronavirus akalla 8 da gwajinsu ya samu nasara.

Sai dai kungiyoyi masu rajin kare hakkin kasashe marasa karfi sun sha alwashin tabbatar da adalci wajen ganin kowa ya samu wadatar rigakafin, wadanda kawo yanzu suka ce sun yi nasarar sayen allurai miliyan 700 da za su rarraba tsakanin kasashe matalauta 92.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.