Amurka

Mutane miliyan 5 sun kamu da coronavirus cikin mako 1 a Amurka

Wasu jami'an Lafiya da ke kula da masu dauke da coronavirus.
Wasu jami'an Lafiya da ke kula da masu dauke da coronavirus. Medical staff members work in the Intensive Care Unit (ICU) wher

Kungiyar Kula da lafiyar kasashen da ke yankin Amurka ta Arewa ta sanar da cewar mutane miliyan 5 suka kamu da cutar korona a cikin mako guda, kuma akasarin su sun fito ne daga kasashen Amurka da Canada.

Talla

Tun bayan barkewar wannan annoba a yankin, Amurka ta Arewa ta samu mutane miliyan 31 da suka harbu da ita, kuma dubu 787,000 daga cikin su sun mutu, adadin da ke zama rabin mutanen da suka harbu da cutar a fadin duniya.

Daraktar kungiyar Carissa Etienne ta ce a mako guda da ya gabata, an samu mutane kusan miliyan 5 da suka kamu da cutar, sakamakon karuwar sabbin masu harbuwa da ita.

Ya zuwa yanzu cutar ta kashe mutane sama da dubu dari 3 a Amurka, inda kasar ta bi sahun Birtaniya wajen fara yiwa jama'arta rigakafin cutar ta hanyar amfani da nau'in maganin da hadakar kamfanin Pfizer da BioNTech suka samar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.