Coronavirus

Corona ta kashe mutane sama da dubu 500 a Turai

Turai ta zama nahiyar da coronavirus ta fi lakume rayuka a duniya.
Turai ta zama nahiyar da coronavirus ta fi lakume rayuka a duniya. MICHAEL DANTAS / AFP

Sabbin alkaluman hukumomin lafiya sun nuna cewar Turai ta zama nahiya ta farko a duniya da cutar coronavirus ta halaka wa sama da mutane dubu 500, shekara guda bayan barkewar annobar.

Talla

Sabon rohoton hukumomin lafiyar ya nuna cewa a halin yanzu jumullar mutane dubu 500 da 69 ne annobar coronavirus ta halaka a nahiyar Turai kadai, daga cikin sama da miliyan 23 da suka kamu da cutar.

Alkalumma sun nuna cewa a tsawon mako guda kadai sama da mutane dubu 37 ne suka mutu a dalilin annobar ta coronavirus a Turan.

Wannan adadi ya sanya Turai zama nahiyar farko da annobar ta halaka mutane sama da rabin miliyan.

Yankin Latin ko kudancin Amurka da Carribean ke biye da Turan da adadin mutane dubu 477 da 404 da cutar ta aika barzahu, sai kuma Amurka da Canada, inda annobar ta lakume rayuka dubu 321, da 287, sai Asiya da ta rasa mutane dubu 208, da 149.

A Gabas ta Tsakiya mutane dubu 85 da 895 annobar ta Korona ta halaka, yayin da a Afrika ta kashe mutane dubu 57 da 423.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.