Coronavirus

Adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus ya haura miliyan 80

Kwayar cutar coronavirus da aka yi amfani da na'urar komfuta wajen fitar da taswirar ta
Kwayar cutar coronavirus da aka yi amfani da na'urar komfuta wajen fitar da taswirar ta NEXU Science Communication | Reuters

Sabbin alkaluman hukumomin lafiya sun nuna cewar adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a yanzu ya kai miliyan 80 da dubu 145 da 185, yayinda kuma annobar ta halaka jumillar mutane miliyan 1 da dubu 756 da 60 shekara guda bayan barkewarta.

Talla

A makon da ya kare kuwa kididdiga ta nuna cewar akalla mutane dubu 580 ake ganowa sun kamu da cutar kowace rana a fadin duniya.

Turai ce nahiyar da annobar ta fi yiwa ta’adi inda ta lakume rayukan akalla mutane dubu 546, daga cikin sama da miliyan 25 da suka kamu.

Amurka da Canada ke biye da Turai wajen fuskantar kaifin wannan cuta, inda ta kashe mutane dubu 346 da 636 daga cikin miliyan 19 da dubu 479, da 293.

A nahiyar Latin da Carribean mutane miliyan 15 da dubu 139 da 172 suka kamu, daga cikinsu kuma annobar ta halaka akalla dubu 494 da 524.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.