China-EU

China da EU na shirin kulla yarjejeniyar kasuwanci mafi girma

Wasu daga cikin shugabannin kungiyar kasashen Turai EU yayin taro a birnin Brussels.
Wasu daga cikin shugabannin kungiyar kasashen Turai EU yayin taro a birnin Brussels. POOL / REUTERS

Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun goyi bayan yunkurin Brussels na shirin kulla yarjejeniyar kasuwanci tsakaninta da China, yarjejeniyar da za ta saukaka harkokin saye da sayarwa tsakanin kasashen 28.

Talla

Yarjejeniyar wadda ake saran ta zama yarjejeniyar kasuwanci mafi karfi tsakanin kasashen tarayyar ta Turai 27 da China mafi karfin tattalin arziki.

Zuwa yanzu dai jakadun kasashen na EU sun fara nuna aminta da yunkurin na Brussels inda jakadar Jamus a kungiyar ke cewa babu alamun samun rashin amincewa daga kowanne bangare na kungiyar zuwa yanzu.

Karkashin yarjejeniyar a wata majiyar Diflomasiyya za a cimma jituwa don kawo karshen zargin bautarwar da ake kan China game da wasu ma’aikatan kamfanoni mallakinta.

Wannan na zuwa mako guda bayan Ma’aikatar harkokin wajen China ta sanar da cewa ana gab da kai wa matakin karshe wajen cimma yarjejeniyar kasuwanci tsakaninta da EU wadda za ta taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin bangarorin biyu.

Babban wakilin EU a tattaunawar Adrzej Sados ya ce suna da kwarin gwiwar a kammala cimma jituwa kowanne lokaci daga yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.