Trump-Amurka

Jawabina ga magoya baya bai da alaka da rikicin Capitol- Trump

Shugaban Amurka bai barin gado Donald Trump.
Shugaban Amurka bai barin gado Donald Trump. REUTERS/Leah Millis

Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump ya musanta zargin aikata ba dai dai ba yayin jawabinsa na Larabar makon jiya da masharhanta ke ganin shi ya tunzura magoya bayansa wajen tayar da rikici tare da farmakar ginin Capitol wanda ya kai ga kisan mutane 5.

Talla

Donald Trump wanda ke jawabi ga manema labarai gabanin wata ziyara a jihar Texas don duba katanga kwanaki 8 gabanin karkare wa'adinsa, ya ce manazarta sun yi nazarin jawabina nasa filla-filla kuma sunyi imanin babu wata alaka tsakanin jawabin da rikicin na Capitol.

A ranar 6 ga watan Janairu gaban dimbin magoya bayansa a birnin Washington Donald Trump cikin jawabinsa ya bukace su da su yi tattaki zuwa majalisar kasar don ceto Amurka, bayan da ya jaddada musu cewar an tabbas an tafka magudi wajen sauya sakamakon zaben kasar na watan Nuwamba.

Jim kadan bayan kalaman na Donald Trump ne dubban magoya bayan nasa suka farwa ginin na Capitol tare da kutsa kai cikin majalisar da nufin kalubalantar nasarar Joe Biden rikicin da ya kai ga asarar rayukan mutane 5 baya ga jikkatar wasu da dama.

Da ya ke mayar da martani kan matakin kamfanonin Twitter da Facebook da suka dakatar da shi ya bayyana dakatarwar a matsayin mafi munin bala'i, yayinda ya bayyana shirin tsigeshi da Majalisun kasar ke yi a matsayin abin dariya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.