Amurka-Honduras

Masu neman mafaka sun fara tattaki daga Honduras zuwa Amurka

Wasu daga cikin 'yan ciranin da ke kokarin shiga Amurka daga Guatemala.
Wasu daga cikin 'yan ciranin da ke kokarin shiga Amurka daga Guatemala. REUTERS/Jorge Cabrera

Wani sabon ayarin dubunnan masu neman mafaka a Honduras sun fara tattakin da zai dauke su lokaci mai tsayi tare da shafe tsawon nisa ta hanyar ratsa kasashen Guatemala da Mexico don kai wa ga Amurka da nufin samun ingantacciyar rayuwa dai dai lokacin da Joe Biden ke gab shan rantsuwar fara aiki.

Talla

Ayarin farko da ke dauke da mutane 300 sun fara tattakin daga yammacin jiya Alhamis daga San Pedro Sula birni na biyu mafi girma a Honduras inda suka nufaci Corinto da ke kan iyakar Guatemala tazarar kilomita 100 daga Arewa maso yammaci.

Ayarin wadanda suka hada tawaga daban-daban dukkaninsu na sanya da kyallen rufe hanci da baki don kariya daga coronavirus haka zalika dauke da tutar Hondura.

Wata Uwa Amanda da ke dauke da danta mai shekaru 10 cikin Ayarin, ta ce tana da yakinin sabon shugaban kasar Amurka Joe Biden zai taimaka wajen basu mafaka a cikin kasar.

Baya ga Ayarin na farko wata tawagar ta mutane dubu 3 daban ta fara haduwa a birnin na San Pedro Sula wadda itama za ta bi sahun ayarin farko a yau Juma’a don tunkarar Amurka cike da saran samun mafaka.

Gwamnatin Honduras tuni ta bayar da jami’an tsaro dubu 7 da basu bayar da kulawa ga ayarin ‘yan ciranin har zuwa kan iyakar Guatemala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.