Rasha-Amurka

Rasha ta fice daga yarjejeniyar sararin samaniya

Shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha. REUTERS

Rasha ta bi sahun Amurka wajen ficewa daga yarjejeniyar sararin samaniya ta Open Skies treaty wadda ta kulla da manyan kasashen Duniya tun 1992, yarjejeniyar da ta bai wa kasashen da ke cikinta damar shawagi da jiragen bincike a sararin samaniyar juna.

Talla

Yarjejeniyar ta Open Skies wadda aka kulla cikin shekarar 1992 ta kuma fara aiki a 2002 ta kunshi ilahirin kasashen Turai, kasashen tsohuwar tarayyar Soviet, baya ga Canada da Amurka, wadda ta sahalewa mambobin da ke cikinta yin shawagi a sararin samaniyar juna don gudanar da bincike kan harkokin tsaro da leken asirin juna kan makaman da su ke kerawa.

Tun a bara ne Amurka ta fice daga yarjejeniyar bayan zargin Rasha da kumbiya kumbiya a cikinta, baya ga karya wasu ka’idoji da yarjejeniyar ta kunsa.

Ma’aikatar harkokin wajen Rasha da ke sanar da matakin ta ce Moscow ta yi iyakar kokarinta wajen shawo kan Amurka don ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar amma Washington ta yi watsi da bayanan da ta aika mata.

Sanarwar ma’aikatar ta zargi Amurka da kafa hujja da bayanan karya da suka kai ta ga ficewa daga yarjejeniyar.

A bara, gwamnatin Donald Trump ta zargi Rasha da kin bai wa wasu jiragen bincike izinin shawagi a sararin samaniyarta haka zalika ta kulle wasu sassa atisayen Soji da ta ke gudanarwa a asirce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.