Annobar Korona ta lakume rayuka sama da miliyan 2

'Yan  uwan wani mutun da annobar Korona ta halaka, yayin kokarin binne gawarsa a birnin New Delhi na kasar India
'Yan uwan wani mutun da annobar Korona ta halaka, yayin kokarin binne gawarsa a birnin New Delhi na kasar India Danish Siddiqui/Reuters

Adadin mutanen da annobar coronavirus ta kashe a fadin duniya ya zarce miliyan 2, kamar yadda sabbin alkaluman hukumomin lafiya suka nuna.

Talla

Bayan shafe shekara guda da bullarta a kasar China, a yanzu cutar ta lakume rayukan mutane miliyan 2 da dubu 66, daga cikin miliyan 93 da dubu 321 da 70 da suka kamu da cutar.

A matakin nahiya annobar ta fi yiwa Turai barna, inda ta kashe mutane dubu 650 da 560 jumila, biye kuma nahiyar Latin da yankin Carribean ne da suka rasa mutane dubu 542 da 410.

A matakin kasashe kuwa, akalla mutane dubu 389 har da 581 cutar ta halaka a Amurka kadai, sai Brazil da ta kashewa mutanen dubu 207 da 95, yayin da a India akalla dubu 151 da 918 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.