Coronavirus

WHO ta hana kasashe tilastawa matafiya nuna shaidar rigakafin Korona

Headikwatar hukumar Lafiya ta Duniya WHO.
Headikwatar hukumar Lafiya ta Duniya WHO. Fabrice Ciffrini / AFP/Getty Images

Kwamitin kar ta kwana na hukumar lafiya ta duniya WHO, ya bukaci hukumomin kasashe da su gaggauta bincike mai zurfi kan sabbin nau’ikan cutar coronavirus da suke yaduwa cikin gaggawa, wadanda tuni suka bazu zuwa akalla kasashe 50, bayan soma bayyana a Birtaniya, Afrika ta Kudu da kuma Brazil.

Talla

A karshen taron masu ruwa da tsakin da ta jagoranta, hukumar WHO ta kuma ki amincewa da kudurin wasu kasashe na neman tilastawa matafiya nuna shaidar karbar rigakafin Korona baya ga na gwajin cutar.

A yayin da yawan rayukan da annobar ta lakume ya zarce miliyan 2 a ranar Juma'a  15 ga watan Janairu, hukumar lafiya ta duniya ta bukaci kowace kasa ta fara aiwatar da shirin allurar rigakafin cutar ga al'ummarta cikin watanni 3 masu zuwa.

A rahotonta na mako mako, hukumar lafiya ta duniya tace sabon nau’in Korona da ta fara bulla a Birtaniya ya yadu zuwa kasashe 50, yayinda kuma wadda aka gano a Afrika ta Kudu ta bazu a kasashe 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.