Manyan kasashe na danne kanana a wajen rabon rigakafin Korona - WHO

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. Christopher Black / World Health Organization / AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana daf da shiga wani mummunan hali na rashin kyautata wa juna, idan har kasashe masu arziki za su ci gaba da handame alluran rigakafin cutar Covid 19 da aka samar, a daidai lokacin da cutar ta kashe sama da mutane miliyan 2 a fadin duniya, duk kuwa da sanin cewa matalautan kasashe za su shiga kunci.

Talla

Shugaban hukumar Lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya caccaki halin son kai da kasashe masu kumbaar susa ke nunawa, yana mai yin kakkausar suka a kan kamfanonin da ke samar da alluran rigakafin saboda yadda suke neman amincewa daga manyan kasashe, maimakon su mika sakamakon bincikensu ga Hukumarsa don samun amincewar amfani da su a duniya baki daya.

A wani jawabi da ya gabatar a taron majalisar zartaswar hukumar a Geneva, shugaban hukumar lafiyar ya ce, alkawarin tabbatar da daidaito a tsakanin kasashe wajen rabon alluran rigakafin cutar Covid 19 na fuskantar barazana.

Tedros ya ce, ya zuwa yanzu, an yi wa mutane miliyan 39 rigakafi a kasashe masu karfin tattalin arziki 49, a yayin da aka samar da allurar rigakafin mutane 25 ne kawai a wata kasa mara karfin tattalin arziki, yana mai karin haske cewa ba miliyan 25, ba kuma dubu 25 ba.

Ya karkare da cewa ko kasashen da suka bayar da tabbacin cewa za a yi raba daidai idan aka samu rigakafi su na nuna son kai ta wajen fififta kansu, a daidai lokacin da cutar ke ci gaba da lakume rayuka a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.