Amurka

Democrat na son Biden ya gaggauta sauya tsarin bayar da mafaka na Trump

Zababben shugaban Amurka Joe Biden.
Zababben shugaban Amurka Joe Biden. AP Photo/Andrew Harnik

Sanatocin Jam’iyyar Democrat na son zababben shugaban Amurka Joe Biden da ke shirin shan rantsuwar kama aiki a gobe Laraba, ya taka rawar gani wajen sauya dokokin bayar da mafaka ga ‘yan kasashen tsakiyar Afrika masu shigowa kasar don neman rayuwa mai inganci.

Talla

Wani rahoto da Democrat ta fitar ta ce batun bayar da mafakar ga ‘yan tsakiyar Amurka zai zamo doka ta farko da Biden zai yi amfani da karfin ikon da kundin tsarin mulki ya bashi wajen sauyawa.

Cikin shekarar 2019 ne Amurka ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar ‘yan cirani tsakaninta da kasashen tsakiyar Amurkan da suka kunshi El Salvador Honduras da kuma Guatemala, yarjejeniyar da za ta taimaka wajen rage yawan ‘yan kasashen 3 da ke kwararowa iyakar Amurka ta kudu.

Yarjejeniyar wadda aka sanyawa suna ACA tun bayan fara aikinta ta hana ‘yan ciranin shiga Amurka kai tsaye, inda ta yi tanadin fara aikewa da bukatar neman mafaka yayinda za su jira sakamakon bukatar ta su a cikin kasashensu, maimakon yadda aka saba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.