Amurka

Biden yayi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Amurka na 46

Joe Biden yayin rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Amurka na 46.  20/1/2021.
Joe Biden yayin rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Amurka na 46. 20/1/2021. REUTERS/Kevin Lamarque

Yanzu haka ana can ana bikin rantsar da zababben shugaban Amurka Joe Biden a massayin shugaban kasa na 46, tare da mataimakiyar sa Kamala Harris a Majalisar dokokin Amurka.

Talla

Bikin dake gudana a Majalisar dokoki kamar yadda aka saba, shine irin sa na farko da shugaba mai barin gado yaki halarta a cikin shekaru 150, ganin yadda shugaba Donald Trump ya haure takalman sa ya tashi zuwa Florida, bayan yayi jawabi a cibiyar soji ta ‘Joint Base Andrews’ inda ya shaidawa magoya bayan sa cewa zai sake dawowa ta wata hanyar, bayan nasarorin da yace ya samu.

A karon farko shugaban mai barin gado ya bayyana fatan alheri ga gwamnati mai shigowa ba tare da kiran sunan shugaba Joe Biden ba.

Mai magana da yawun sabon shugaban Judd Deere yace Donald Trump ya barwa Joe Biden Wasika a fadar shugaban kasa.

Daga cikin manyan bakin dake halartar bikin rantsar da shugaba Biden da Kamala Harris harda tsohon shugaban kasa barack Obama da uwargidan sa Michelle da Bill Clinton da uwargidan sa Hillary.

Damian tsaro 25,000 aka gripe domin fus kantar duk wata barabana daga masu tada bankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.