Amurka

Manufofin Trump da suka sauya alkibilar Amurka

Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump REUTERS/Carlos Barria

Yau shugaba Donald Trump ke karkare zangonsa na mulkin Amurka da ya kwashe shekaru 4 yana kai, inda zai mika ragamar tafiyar da kasar ga zababben shugaban kasar Joe Biden.

Talla

Trump wanda ya kada Hillary Clinton a zaben shekarar 2016 ya sauya alkiblar Amurka wajen fafatawa da kawayen ta dangane da abinda ya shafi kasuwanci da kuma tsaro, inda ya rika sa kafar wando guda da kasashen Turai wadanda ya zarga san kansu.

Bashir Ibrahim Idris ya duba wasu daga cikin manufofin Trump da ba za a manta da su ba.

Yadda shugaba Trump ya sauya alkibilar Amurka

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.