Sabon nau'in cutar Korona ya bazu zuwa sama da kasashe 60
Wallafawa ranar:
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO tace sabon nau’in cutar Coronavirus mai saurin yaduwa da ta soma bayyana a Birtaniya ya bazu zuwa sama da kasashe 60.
Hukumar ta WHO ta kuma ce sabon nau’in cutar ta Korona da ya bayyana a Afrika ta Kudu ya yadu zuwa kasashe 23 a yanzu.
Rahoton na zuwa ne a yayinda annobar ta lakume rayukan mutane sama da miliyan 2 a fadin duniya, daga cikin kusan miliyan 100 da suka kamu da cutar, shekara guda bayan bullarta a birnin Wuhan na kasar China.
Gano magungunan rigakafin annobar ta Korona da kamfanonin Pfizer, BioNTech, AstraZeneca, Moderna da kuma Jami’ar Oxford suka yi a karshen shekarar 2020 ya baiwa hukumomi kwarin gwiwar fatan kawo karshen cutar a nan kusa.
Sai dai bayyanar sabbin nau’ikan cutar a baya bayan nan, ya haifar da fargaba kan ko alluran rigakafin da aka samar za su yi tasiri wajen dakile su, a dai dai lokacin da hukumomin kasashe a sassan duniya suka tsaurara matakan takaita walwalar jama’a don yakar annobar da sake barkewa a zango na biyu.
A ranar Laraba China da tafi kowace kasa samun nasarar dakile cutar, ta sake kakabawa al’ummar Beijing dokar kullen hanasu fita daga birnin, saboda sake bayyana annobar a yankin Daxing dake kudancin babban birnin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu