Amurka

Ina aka kwana kan batun tsige Trump a majalisar dattawar Amurka?

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Carlos Barria

Shugabar Majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi taki bayyana lokacin da zata mikawa Majalisar Dattawa takardun bukatar tsige tsohon shugaban kasa Donald Trump domin ganin ya fuskanci hukunci, duk da adawar da Jam’iyyar Republican keyi kan bukatar, yayın da sabon shugaban kasa Joe Biden ya bukaci hadin kan jama’a.

Talla

Pelosi tace tsohon shugaban ya aikata babban laifi wajen tinzira jama’a suyi bore da kai hari Majalisar, inda har mutane 5 suka mutu, saboda haka babu dalilin da za’a kauda ido ba tare da daukan mataki akan sa ba.

Shugaban 'Yan Jam’iyyar Republican a Majalisar Mitch McConnell ya bar kofa bude wajen ganin an hukunta tsohon shugaban, amma Sanata Lindsey Graham na hannun daman tsohon shugaban yace allura na iya tono garma wajen binciken tsohon shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.