Amurka

Adadin masu dauke da Korona a Amurka sun zarta miliyan 5

Masu kulawa da cutar korona a kasar Amurka
Masu kulawa da cutar korona a kasar Amurka REUTERS

Akaluman jami’ar John Hopkins sun nuna cewa zuwa yanzu akwai Amurkawa fiye da miliyan 25 da suka harbu da cutar Covid-19 a sassan kasar tun bayan bullarta a bara.

Talla

Cikin bayanan da jami’ar ta Johns Hopkins ke fitarwa kan halin da ake ciki game da cutar ta Covid-19 a Amurka, ta ce cutar ta kama mutum miliyan 24 da dubu 3 da 695 zuwa yanzu kwanaki kalilan bayan jumullar wadanda ta kashe ya kai dubu dari 4 a kasar, mafi karfin tattalin arziki.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden da ya sanar da kaddamar da yaki kan cutar bayan amincewa da tallafin rage radadin cutar na dala tiriliyan 1 da biliyan 9, ya ce yana fatan yiwa al’ummar kasar miliyan 100 allurar rigakafin cikin kwanaki 100 na farkon mulkinsa, yayinda ya bukaci Amurkawa su rungumi dabi’ar sanya kyallen rufe hanci na kwanaki darin.

Yanzu haka dai kasashen Duniya na rige-rigen yiwa jama’arsu allurar rigakafin cutar ne don dakile barnar da ta ke ci gaba dayi, inda Vivek Murthy mashawarcin Biden kan lafiya, ke cewa alluran miliyan 100 fandisho ne na yakar cutar da gwamnatinsu za ta gwabza, don hana tasirin sabuwar nau’in coronar da masana ke hasashen sake zuwanta a nan gaba.

A cewar Vivek zabi ne ga Amurkawa wajen bayar da hadin kai don cikar kudirin da suka sanya na yakar cutar daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.