Duniya-Coronavirus

Coronavirus ta tilastawa kasashe da dama sake rufe iyakokinsu

Yadda filin jiragen sama na Nikola Tesla dake Belgrade babban birnin Serbia ya kasance babu mutane, saboda matakin rufe iyakokinta domin dakile yaduwar cutar Coronavirus.
Yadda filin jiragen sama na Nikola Tesla dake Belgrade babban birnin Serbia ya kasance babu mutane, saboda matakin rufe iyakokinta domin dakile yaduwar cutar Coronavirus. REUTERS/Marko Djurica

Hukumomin kasashe sun soma sake daukar matakan rufe iyakokinsu don dakile barazanar annobar coronavirus da taki yiwa duniya sassauci wajen lakume rayuka gami da bazuwa tamkar wutar daji.

Talla

Yau Litinin Amurka ta tabi sawun Faransa, Isra’ila da kuma Sweden da suka rufe iyakokinsu ga matafiya daga Birtaniya, Brazil, Ireland da kuma wasu karin kasashen Turai da dama, saboda dakile yaduwar sabon nau’in cutar Korona da ya soma bayyana a Afrika ta Kudu da kuma Birtaniya.

Tsaurara matakan yaki da Koronar dai na zuwa ne bayan da shugaban kasar Mexico Andres Manuel Obrador ya zama fitaccen mutum da a baya bayan nan, ya kamu da cutar.

A birnin Washington, shugaban Amurka Joe Biden ya sake rufe iyaka ga matafiyan da ba ‘yan asalin kasar ba, daga kasashen Brazil, Birtaniya, Ireland da kuma Afrika ta Kudu, bayan da a makon jiya ya kafa dokar tilasatawa Amurkawa sanya takunkumin rufe baki da hanci.

Kawo yanzu annobar Korona ta halaka mutane sama da miliyan 2 da dubu 100, daga cikin kusan miliyan 99 da suka kamu da cutar a fadin duniya, annobar kuma tafi ta’adi a Amurka bayan halaka sama da mutane dubu 400 a kasar kadai, daga cikin sama da miliyan 25 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.