Kusan mutane dubu 500 ne matsanancin sauyin yanayi ya kashe - Rahoto

Amfanin gona na mutuwa sakamakon canjin yanayi.
Amfanin gona na mutuwa sakamakon canjin yanayi. RFI/Agnieszka Kumor

Wani Binciken masana kimiya yace tsananin zafin da aka gani a shekaru 20 da suka gabata, yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan rabin miliyan a fadin duniya.

Talla

Binciken ya ce wannan matsala dake haifar da guguwa mai karfi da ambaliya da yanayin zafi yafi kamari ne a kasashe masu tasowa, saboda rashin ingancın hanyoyin tinkarar matsalolin.

Kungiyar Germanwatch da ta gabatar da wannan rahoto ta ce wadannan matsaloli da aka fuskanta sun yi sanadiyar asarar kudin ya kai sama da triliyan biyu da rabi, baya ga rasa dimbin rayuka a cikin wannan karnin.

Binciken wanda ya nuna mutuwar mutane kusan 480,000 tun daga shekara ta 2000, ya bayyana kasashe irin su Puerto Rico da Myanmar da kuma Haiti a matsayın wadanda suka fi fuskantar radadin matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.