Amurka

Masu adawa da Joe Biden na shirin kai hare-hare a Amurka - Gwamnati

Allo dauke da alamun Donald Trupm da na Joe Biden
Allo dauke da alamun Donald Trupm da na Joe Biden Reuters

Gwamnatin Amurka ta tsaurara matakan tsaron ta a cikin gida sakamakon rahotan binciken da ya nuna cewar wasu masu tsatsauran ra’ayi dake adawa da shugabancin Joe Biden na shirin kaddamar da hare hare.

Talla

Ma’aikatar cikin gidan kasar tace bayanan da suka samu daga wadannan masu tsatsauran ra’ayi dake adawa da sabuwar gwamnati da kuma mika mulkin da akayi, ya nuna cewar ana yaudarar su da labaran karya domin tinzira su wajen ganin sun haifar da sabon tashin hankalı.

Sanarwar hukumar yaki da ta’addanci yace ana iya fuskantar wadannan hare hare a koda yaushe bayan kama aikin sabon shugaban kasa, duk da yake babu bayanai dangane da takamammen lokacin kai harin.

Gwamnatin kasar tace ana cigaba da samun hare hare a cikin ‘yan kwanakin nan kuma ta damu da yadda wasu mutane da basu jin dadin sakamakon zaben kasar ba ke yaudarar mangoya bayan su domin tada hankalın.

Sanarwar tace tun daga shekarer da ta wuce ake fuskantar irin wadannan barazana da ake danganta su da annobar korona da kuma kayen da Donald Trump ya sha a zaben watan Nuwamba da cin zarafın Yan sanda da kuma shirin korar baki.

Gwamnatin tace harin da magoya bayan tsohon shugaban kasa Donald Trump suka kai Majalisar dokoki na iya karfafa wasu cigaba da kai wasu hare hare kan ‘yan siyasa da jami’an gwamnati da kuma gine gine.

Ya zuwa yanzu an kama akalla mutane sama da 150 tun bayan harin da aka kai Majalisar dokoki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.