Rasha-Amurka-Iran

Rasha ta bukaci Amurka ta cirewa Iran takunkuman karya tattalin arziki

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. REUTERS/Maxim Shemetov TPX

Kasar Rasha ta ce kallo ya koma wajen shugaban Amurka Joe Biden hajen yin yunkurin farko domin ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran da ke neman rugujewa.

Talla

Ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov ya bukaci Amurka ta cirewa Iran takunkumin karya tattalin arzikin da ta dora mata, domin bude kofar sasantawa da kasar dangane da wannan yarjejeniyar.

Lavrov ya ce Rasha da Iran na kan matsayi guda dangane da shirin kare yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015 da aka kulla.

Sai dai Faransa ta ce kallo ya koma wurin Iran domin nuna cewar da gaske kasar ta ke wajen aiwatar da yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.