Amurka

Zubar dusar kankara ta tilasta dakatar da hada-hada a gabashin Amurka

Hukumomi a kasar sun aike da tarin motocin kwashe kankarar dan baiwa jama'a sukunin ci gaba da hada-hada.
Hukumomi a kasar sun aike da tarin motocin kwashe kankarar dan baiwa jama'a sukunin ci gaba da hada-hada. REUTERS/Rickey Rogers

Zubar dusar kankara mai yawa ya haifar da matsaloli sosai a Gabashin Amurka abin da ya tilasta rufe makarantu da soke sauka da tashin daruruwan jiragen sama da kuma soke allurar rigakafin coronavirus a birnin New York.

Talla

Hukumar da ke kula da yanayi ta kasar Amurka ta gabatar da gargadi mai karfi tsakanin Virginia zuwa Maine mai dauke da miliyoyin jama’a saboda yadda dusar kankarar mai dauke da iska ta dinga zuba.

Jihar New York ta kafa dokar ta baci saboda lamarin, inda aka hana jama’a tafiye tafiyen da basu da muhimmanci, yayin da aka kwashe yara kanana zuwa wata cibiyar domin kula da lafiyar su.

An tura tarin motocin da ke dauke da gishiri da masu kwasar dusar kan tituna, a daidai lokacin da Magajin Garin Birnin New York Bill de Blasio ya umurci dalibai su zauna gida.

Hukumomi sun soke sauka da tashin jiragen sama da yawan su ya kai 1,600 a tashoshin jiragen saman New York da Boston da Philadelphia da Washington, yayin da wasu kamfanonin jiragen kuma suka soke tashin jiragen su a tashar La Guardia da JFK, sai kuma tashar Newark Liberty da ta soke kashi 71 na tashin jiragen daga cikin ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI