US -IRAN

Amurka na shirin cirewa Iran takunkumi

Shugaban juyin juya halin kasar Iran Ayatoullah Ali Khamenei sanye da kellen rufe hanci da baki saboda kariyar cutar korona
Shugaban juyin juya halin kasar Iran Ayatoullah Ali Khamenei sanye da kellen rufe hanci da baki saboda kariyar cutar korona Reuters

Amruka ta dauki wasu jerin matakai uku dangane da kasar Iran, a kokarin da kasshen Turai ke yi wajen ganin ta koma tattaunawar sake farfado da yarjejeniyar Nukliyar da ta cimma da kasar, kafin cikar wa’adin da Iran ta diba na takaita shigar jami’an hukumar samar da makamashin nukliya ta Majalisar Dinkin Duniya shiga cibiyoyin nukliyarta.

Talla

Bayan wani zaman taro ta hoton bidiyo da ya hada ministocin harakokin wajen Faransa da britanniya da Jamus da kuma Amurka ne,  hukumomin Washington suka bayyana amincewa da tayin da Kungiyar Tarayyar Turai ta yi mata na shiga tattaunawa da gwamnatin Tehran domin sake farfado da yarjejeniyar nukliyar ta 2015.

A yayin da take maida martani bayan yinkurin tattaunawar da gwamnatin sabon shugaban Amruka Joe Bide yau Jumma'a, kasar Iran ta sake jadda kiranta ga Amruka da ta dage mata illahirin takunkuman kariyar tattalin ariziki da tsohon shugaba Donald Trump ya kakaba mata.

A cikin wani sako ta shafin twita ministan harakokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya ce da zarar  Amruka ta dage mata jerin takunkuman da Donald Trump ya kakaba mata  ba tare da gindaya wasu sharudda ba, to kuwa nan take Téhéran za ta  tsaida aiki da duk wasu matakai da suka sabawa yarjejeniyar nan take.

Gwamnatin Kremlin ta kasar Rasha ta bayyana farin cikinta da aniyar Amrukan na sake farfado da aiki da yarjeniyar nukliyar ta 2015 da Donald Trump ya fitar da kasar a ciki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI