Kotun kolin Amurka ta yi umarnin bincikar takardun harajin Trump
Wallafawa ranar:
Kotun Kolin Amurka ta amince da bukatar bai wa masu gabatar da kara takardun shaidar biyan harajin tsohon shugaban kasa Donald Trump sabanin karar da ya shigar domin ganin an hana su ganin takardun.
Lauyoyin Trump sun sake rugawa kotun ne inda suke bukatar kariya daga gabatar da takardun harajin, amma kotun tace Babban lauyan Manhattan na iya karbar takardun wanda tsohon shugaban baya so jama’a su gani.
Batun kaucewa biyan harajin Trump ya zama abin cece kuce lokacin zaben da ya gabata, sakamakon rahotannin da ke nuna cewar tsohon shugaban ya kwashe shekaru 8 baya biyan haraji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu