Faransa-China

Faransa ta caccaki cin zarafin da China ke yi wa al'ummar Uighur

Jami'an tsaron China na sintiri a yayin da wasu daga cikin 'yan kabilar Uighur suka fito daga Masallaci
Jami'an tsaron China na sintiri a yayin da wasu daga cikin 'yan kabilar Uighur suka fito daga Masallaci AFP/File

Gwamnatin Faransa ta caccaki abin da ta kira tsararren cin zarafin da China ke yi wa tsirarrun al’ummar kabilar Uighur da ke kasar.

Talla

A yayin jawabi ta kafar bidiyo a zauren Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Geneva, Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Yves Le Drian ya ce, shaidu da takardun da aka tattara daga yankin Xinjiang sun nuna yadda ake murkushe‘yan kabilar Uighur da ke China.

Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama sun yi amanna cewa, akalla  ‘yan kabilar Uighur miliyan guda da kuma wasu tsirarun Musulmai masu magana da harshen Turkic aka garkame a sansanonin da ke yankin yammacin Xinjiang.

Le Drian ya bayyana Xinjiang a matsayin daya daga cikin wuraren da suka yi kaurin-suna wajen danne hakkokin al’umma a cikin shekarar 2020.

A bangare guda, Ministan Harkokin Wajen na Faransa ya lissafa yunkurin kisan da aka yi kan jagoran ‘yan adawar Rasha Alexei Navalny ta hanyar dirka masa guda, a cikin jerin cin zarafin bil’adama da aka gani a baya-bayan nan.

Kazalika Ministan ya tabo batun murkushewar da jami’an tsaro suka yi wa masu zanga-zangar tabbatar da Demokuradiya a Belarus da kuma yake-yaken da ake ci gaba da fama da su a Syria da Yemen da kuma juyin mulkin Myanmar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.