Gwamnatin Biden ta kaddamar da harin farko a Syria
Wallafawa ranar:
Sojojin Amurka sun kaddamar da farmaki kan ‘yan tawayen da ke samun goyon Iran a gabashin Syria, inda mutane 22 suka rasa rayukansu, yayin da gwamnatin shugaba Joe Biden ta bayyana farmakin a matsayin gargadi.
Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta bayyana farmakin a matsayin gargadi daga sabuwar gwamnatin Amurka bayan hare-haren makaman roka da aka kai wa sojojin na Amurka da ke Iraqi.
A karon farko kenan da Amurka ta kai hari tun bayan darewar Biden karagar mulki makwanni biyar da suka gabata, yayin da Pentagon ke cewa, harin ya kuma lalata kadarori da dama da mayakan masu samun goyon bayan Iran ke amfani da su a gabashin Syria.
Kungiyar da ke Sanya Ido kan Hakkin Bi’adama a Syria ta ce, farmakin ya tawratsa wasu manyan motoci makare da makamai da suka taso daga Iraqi a kusa da kan iyakar garin Albu Kamal.
Kazalika harin ya yi raga-raga da shigen da mayakan suka kafa a kan iyakar garin na Albu Kamal.
Tuni gwamnatin Syria ta yi tur da wannan harin wanda ta bayyana a matsayin mummunar alama da ta so daga sabuwar gwamnatin Biden.
Ita ma Rasha wadda ke kawance da shugaba Bashar al-Assad ta fito ta caccaki farmakin na Amurka, tana mai bukatar hukumomin Washinbgton da su mutunta ‘yancin iyakokin kasar ta Syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu