Majalisar Dinkin Duniya

MDD na neman agajin biliyan 2 don wadata Duniya da tukwanen iskar Oxygen

Fiye da mutane miliyan 19 ne yanzu haka ke bukatar iskar ta Oxygen musamman a kasashen yankin Amurka da cutar coronavirus ta fi tsananta.
Fiye da mutane miliyan 19 ne yanzu haka ke bukatar iskar ta Oxygen musamman a kasashen yankin Amurka da cutar coronavirus ta fi tsananta. ORLANDO SIERRA AFP/File

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar annobar corona ta haifar da tsananin karancin iskar Oxygen da marasa lafiya ke bukata a asibitoci, abin da ya sanya majalisar kiran gaggauta tara akalla dala biliyan 1 da miliyan 600 domin shawo kan matsalar da ta shafi duniya baki daya. 

Talla

Rahotannin baya bayan nan da hukumomin lafiya suka fitar sun bayyana cewar annobar ta corona ta dade da haifar da nauyin da ke barazanar durkusar da sha’anin kiwon lafiya a fadin Duniya, musamman a kasashe matalauta, inda tuni asibitocinsu ke fuskantar karancin tukwanen iskar Oxygen da marasa lafiya ke bukata.

A wasu kasashen marasa karfi, tuni yanayin ya kai ga tilastawa iyalai biyan kudade na musamman domin sayawa ‘yan uwansu da cutar corona ta kwantar tukwanen na Iskar Oxygen.

Tun kafin barkewar annobar Korona, bincike ya nuna cewar asibitoci a sassan duniya na fuskantar karancin tukwanen iskar ta Oxygen da ake bukata domin taimakawa marasa lafiya masu fama cutukan irinsu Pneumonia wajen numfashi, cutar da alkaluma suka nuna cewar tana lakume rayukan akalla mutane miliyan 2 da rabi a fadin Duniya.

Corona da Oxygen

Zuwa yanzu kwararru sun bayyana cewa kimanin mutane dubu 500 da ke fama da cutar corona a kasashe masu tasowa na neman agajin gaggawa na takwanen Iskar Oxygen miliyan 1 da 100 a kowace rana, yanayin da yafi kamari a wasu kasashen Afrika 25.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.