Haiti

Mutune 25 sun mutu a Haiti lokacin da Fursunoni 400 suka tsere a kurkuku

Wasu daga cikin fursunoni da jami'an tsaro Haiti suka cafke bayan tsarewa daga kurkuku ranar 27 ga watan Fabairun shekarar 2021
Wasu daga cikin fursunoni da jami'an tsaro Haiti suka cafke bayan tsarewa daga kurkuku ranar 27 ga watan Fabairun shekarar 2021 AP - Dieu Nalio Chery

Hukumomin Haiti sunce, suna neman fiye da fursunoni 200 da suka tsere, kwana guda bayan wani mummunan rikicin a kurkukun da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 25 ciki har da darektan gidan yarin.

Talla

Kamfanin dillancin Labaran Faransa na AFP ta nuna hotonan akalla gawawwaki uku da ke kwance a wajen gidan yarin da kuma wasu fursunonin da aka kame a bayan wata babbar mota, bayan da Kimanin fursunoni 400 suka tsere a ranar Alhamis.

Daya daga cikin fursunoni 400 da aka kame lokacin da suke tserewa
Daya daga cikin fursunoni 400 da aka kame lokacin da suke tserewa AP - Dieu Nalio Chery
"Mutane 25 suka mutu ciki har da fursunoni shida da kuma Sufeto na sashen Paul Hector Joseph wanda ke kula da gidan yarin," Sakataren Sadarwa Frantz Exantus ya ce game da tserewar da aka yi daga gidan yarin da ke wajen babban birnin kasar Port-au-Prince.

"Daga cikin wadanda aka kashe har da wasu basu ji ba basu gani ba, da fursunonin suka kashe a lokacin da suke tserewa."

Kimanin fursunoni 200 har yanzu ba a gansu ba, amma "'yan sanda na aiki tukuru don ganin an dawo da su. Wasu da dauke da anko, ba za su iya yin nisa ba," in ji jami’in.

Cikin fursunonin da suka mutu harda wani shugaban kungiyar ‘yan daba Arnel Joseph, wanda aka kashe a ranar Juma’a a wani shingen bincike yayin da yake tsewa.

Mutane na wuciwa gefen gawar daya daga cikin fursunonin da jami'an tsaro suka harbe har lahira a Haiti
Mutane na wuciwa gefen gawar daya daga cikin fursunonin da jami'an tsaro suka harbe har lahira a Haiti AP - Dieu Nalio Chery
Joseph, wanda ake zargin shine shugaban daya daga cikin manyan kungiyoyin dake aikata laifuka na Haiti, an kama shi a shekarar 2019 kuma ya yi kokarin tserewa daga gidan yarin a watan Yulin da ya gabata bayan da ya tallata shirinsa a wani bidiyo na kafar sada zumunta kwanaki kadan kafin yunkurin.

Yayin da yake zaman wakafi kan hukuncin kisan da aka yanke masa, Joseph ya tsere har sau biyu daga wani gidan yari, a Port-au-Prince, a shekarun 2010 da 2017.

A shekarar 2012, aka bude gidan kurkukun mai tsananin tsaro na Croix-des-Bouquets, wanda kasar Canada ta bada tallafi gina shi, na iya ɗaukar fursunoni 872, kodayake an ninka kusan adadin da ke tsare a wurin kafin tserewar na alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI