Amurka-Coronavirus

Amurka ta amince da ingancin rigakafin Korona na kamfanin Johnson & Johnson

Allurar rigakafin cutar Korona da kamfanin Johnson & Johnson ya samar.
Allurar rigakafin cutar Korona da kamfanin Johnson & Johnson ya samar. AP

Kwararru a Amurka sun amince da ingancin allurar rigakafin cutar Korona da kamfanin magunguna na Johnson & Johnson ya samar.

Talla

A makon da ya kare hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka ta tantance allurar wanda ita ce ta uku da za a baiwa al’ummar kasar bayan rigakafin Pfizer da kuma Moderna.

Sabanin sauran alluran rigakafin da ake bukatar tsikarawa mutane sau biyu, za a rika yiwa mutane ta Johnson & Johnson sau daya ne kawai, wadda masana suka ce tana da tasirin kashi 81 kan dukkanin nau’ikan cutar Korona.

Gwajin kwararrun ya kuma tabbatar da cewar allurar rigakafin Koronar na Johnson and Johnson baya haifar da wasu matsaloli ga lafiya, kamar yadda aka fuskanta yayin gwajin magungunan Pfizer da Moderna a tsakanin wasu tsirarun mutane.

Zuwa yanzu mutane sama da dubu 500 annobar Korona ta kashe a Amurka, yayinda kuma aka yiwa ‘yan kasar kmanin miliyan 65 allurar rigakafin cutar da magungunan Pfizer da Moderna.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI