Yemen - Saudiya

'Yan tawayen Huthi na kasar Yemen sun dauki alhakin yunkurin kai farmaki Saudiya

Mayakan tawayen Huthi yayin gangami nuna adawa da kawance da Saudiya ke jagoranta a birnin Sanaa na kasar Yemen
Mayakan tawayen Huthi yayin gangami nuna adawa da kawance da Saudiya ke jagoranta a birnin Sanaa na kasar Yemen AFP

'Yan tawayen Huthi na kasar Yemen da ke samun goyon bayan Iran sun dauki alhakin harba makami mai linzami makwabciyar su Saudiya kafin a tarwatsa  cikin dare tare da barazanar kai wasu hare-hare, yayin da rikici ke kara kazancewa a kasar Yemen.

Talla

Mayakan Huthi sun zafafa kai farmaki kan Saudiya a dai-dai lokacin da dakarun kawancen da Saudiyya ke jagoranta ke kai hare-haren sama kan 'yan tawaye a arewacin Yemen, a wani yunkuri na dakatar da farmakinsu na kwace iko da garin Marib da ke amtsayin tingan karshe dake hannun gwamnati a arewacin kasar.

Saudiya wacce ke marawa gwamnatin Yemen baya tun shekara ta 2015 - ta  sanar da dakile wani harin makami mai linzami da mayakan na Huthi suka yi nufin harba shi zuwa Riyadh.

Dakile yunkurin kai farmakin da mayakan na Houthi suka yi, na zuwa ne sa’o’i bayan kazamin fadan da ‘yan tawayen suka gwabza da sojojin Yemen a birnin Ma’arib, inda akalla mayaka 50 suka rasa rayukansu daga bangarorin biyu.

Har yanzu dai mayakan na Houthi basu dauki alhakin harba makaman masu linzami kan Saudiya ba, sai dai a baya sun sha yin ikirarin kai hare-hare da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuki kan wasu yankunan kudancin kasar, baya ga yunkurin farwa birnin Riyadh a lokuta da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.