Saudiya-Amurka

Rahoton Amurka kan kisan Kashoggi ya taba martabar Yariman Saudiya

Yarima mai jiran gado na Saudiya Muhammad bin Salman.
Yarima mai jiran gado na Saudiya Muhammad bin Salman. AFP - FAYEZ NURELDINE

Matakin shugaban Amurka Joe Biden na wallafa rahoton hukumar leken asirin kasar kan kisan fitaccen dan jarida Jamal Kashoggi da ya nuna Yarima mai jiran gado na Saudiya Muhammad Bin Salman ke da hannu a umarnin kisan da kuma batar da gawar, ya fara fito da tsamin alakar kasashen biyu karara gaban idon Duniya, yayinda a bangare guda ya ke matsayin barazana ga daukakar Yariman.

Talla

Majiyoyi da dama na ruwaito yadda rahoton na Amurka ya shafi hatta daukakar Yariman na Saudiya da ke matsayin magajin iko a kasar mai arzikin man fetur, ko da ya ke tuni Saudiyan ta yi watsi da rahoton da ta ce baya kan gaskiya.

Biden wanda ya alakanta Trump da masaniya kan kisan na Kashoggi a ranar 2 ga watan Oktoban 2018, ya ce kisan ya bayyana gazawar Muhammad bin Salman tsakanin takwarorinsa shugabannin kasashen gabas ta tsakiya.

Yariman wanda aka fi sani da MBS da ke matsayin aboki ga tsohon shugaban Amurka Donald Trump take-takensa tun gabanin zaben Amurka na 2020 ya nuna karara baya tare da jam’iyyar Democrat.

A cewar sakataren harkokin wajen amurka Antony Blinken Shugaban kasar Joe Biden na fatan gyatta alaka tsakanin kasar da Saudiya, said ai baya goyon bayan wasu manufofin Yariman.

Har zuwa yanzu dai Amurka ba ta sanar da Shirin sanya takunkumi kan Saudiya ba, sai dai Biden a wani jawabinsa ga fadar White House bayan fitar da rahoton, ya ce yana Shirin yin wata ganawar sirri tsakaninsa da Yariman na Saudiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.