Isra'ila-Falasinu

ICC na bincike kan yakin da Isra'ila ta kaddamar wa Falasdinawa

Babbar mai shigar da kara ta kotun ICC, Fatou Bensouda.
Babbar mai shigar da kara ta kotun ICC, Fatou Bensouda. Bas Czerwinski/Pool via REUTERS/File Photo

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC ta fara binciken laifukan yaki da kuma mamayar da Isra’ila ta yi wa yankunan Falasdinawa, abin da ya tayar da rigingimun da suka dauki hankalin duniya.

Talla

Babbar mai gabatar da kara Fatou Bensouda ce za ta jagoranci gabatar da karar mai cike da sarkakiya da ke zargin Isra’ila da kaddamar da yaki kan Falasdinawa musamman lokacin yakin zirin gaza a shekarar 2014.

Sai dai Isra’ila wadda ba ta cikin mambobin kotun ta ICC ta bayyana binciken a matsayin cin zarafi da kuma karan- saye ga doka.

Amma abin ba haka yake ba ga Falasidanawa da suke nuna farincikinsu da fara wannan bincike, tare da bukatar kotun da ta gaggauta yanke hukunci.

Rahotanni sun bayyana cewa, akalla Falasdinawa dubu 2 da da 500 ne suka hallaka a yayin wata arangama tsakanin jami’an tsaron isra’ila da kuma farafen hula daga bangaren Falasdinawa a shekarar 2014.

 

Hayaki da kura sun turnuke sararin samaniya a wani hari da Isra'ila ta kaddamar a zirin Gaza a shekarar 2014.Smoke, dust and debris rise after an Israeli strike hits in Gaza City, northern Gaza Strip, Tuesday, Aug. 26, 2014. (AP Photo/Adel Hana)
Hayaki da kura sun turnuke sararin samaniya a wani hari da Isra'ila ta kaddamar a zirin Gaza a shekarar 2014.Smoke, dust and debris rise after an Israeli strike hits in Gaza City, northern Gaza Strip, Tuesday, Aug. 26, 2014. (AP Photo/Adel Hana) AP - Adel Hana

Shi kuwa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, tun watan da ya gabata ya caccaki alkalan kotun bisa damar da suka bayar ta fara gudanar da binciken.

Da ma  Falasdinawa sun dade suna jiran zuwan lokacin da za a bude damar binciken da suke ganin karara israila na yunkurin murkushe su ne.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.