Kasashen Duniya sun tafka sarar ton biliyan 1 na abinci a 2019- MDD
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya ta ce an tafka asarar kashi 17 cikin 100 na yawan abincin da ke isa ga mutane a fadin duniya kwatankwacin kusan ton biliyan 1 a shekarar 2019. Rahoton ya ce an tafka gagarumar hasarar ce bayan da gidaje, shaguna, da manyan masana’antu suka rika zubar da kayayyakin abincin da suka lalace ko suka rube.
Kididdigar da rahoton Majalisar Dinkin Duniyar ya wallafa ta nuna cewar idan aka rarraba yawan abincin da Duniya ta tafka asarar shi a shekarar ta 2019, zuwa cikin manyan motoci masu daukar nauyin ton 40-40, kwatankwacin yawan motocin dakon kayan da za su dauki jumillar abincin da za su iya zagaye duniya har ninki 7.
Majalisar ta kuma bayyana cewa yanzu haka kusan mutane miliyan 700 ne ke kwana cikin yunwa kowace rana a fadin duniya.
Zalika a kowace rana ana zubar da abincin da yawansa ya kai kilogram 121, kuma rabin adadin wato kilo 74 gidaje ke zubdawa.
Majalisar Dinkin Duniya ta tattara rahoton na ta ne bayan gudanar da bincike a tsakanin kasashe 54, da suka hada da matalauta, masu tasowa da kuma masu arziki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu