Jami'an tsaro Myanmar sun ci gaba da mukushe masu zanga-zanga

Yadda zangar-zangar adawa da juyin mulki a Myanmar ta zama tarzoma
Yadda zangar-zangar adawa da juyin mulki a Myanmar ta zama tarzoma STR AFP

Jami’an tsaro a Myanmar sun sake harbe wani mai zanga-zangar adawa da juyin mulki har lahira jiya Juma’a, adai-dai lokacin da wakilin Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci Kwamitin Tsaro ya saurari “kiraye-kirayen” ‘yan kasar tare da daukar matakin gaggawa don dawo da dimokiradiyya.

Talla

Duk da karfi da jami’an tsaro ke nunawa domin murkushe masu zanga-zanga da tuni sama da 50 suka mutu daga cikinsu, masu adawa da juyin mulkin na ranar 1 ga watan Fabrairu sun ci gaba da mamaye titunan biranen kasar.

A Mandalay, birni na biyu mafi girma a Myanmar, daruruwan injiniyoyi sun fito kan tituna suna kira da  a saki jagoransu" wato daya daga cikin mukarraban Aung San Suu Kyi, da sojoji suka tsare tun daren farko na kwace mulki.

Wani matashi mai shekaru 26 da ke taimakawa a shingayen da aka kafa a cikin birni don rage hanzarin jami'an tsaro ya mutu bayan da aka harbe shi a wuya, kamar yadda jami'an kiwon lafiya suka shaida wa AFP.

Kisan ya biyo bayan wanda ta fi muni tun bayan soma zanga-zangar wato ranar ranar Laraba, wanda da Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kalla mutane 38 aka kashe yayin da hotuna suka nuna yadda jami’an tsaro suka yi harbi cikin taron jama’a kuma aka ja gawawwakin mutane cikin jini.

'Yan sanda sun kuma harba hayaki mai sa hawaye a kan masu zanga-zangar a garin Dawei da ke kudancin kasar yayin da masu zanga-zangar a babban birnin kasuwanci na Yangon suka nuna turjiya duk da hatsarin da suke fuskanta.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.