Yemen-Houthi

Yemen da 'yan tawayen Houthi sun rasa mayaka 90 a sabon fadan da suka gwabza

Wani yanki na birnin San'a a kasar Yemen da ya fuskanci farmakin jiragen yaki.
Wani yanki na birnin San'a a kasar Yemen da ya fuskanci farmakin jiragen yaki. AP - Hani Mohammed

Rundunar sojin Yemen ta ce mayaka akalla 90 ne suka rasa rayukansu yayin gumurzun da dakarunta suka da ‘yan tawayen Houthi tsawon sa’o’i 24 da suka gabata.

Talla

Sanarwar tace sojojin Yemen 32 ne suka mutu yayin fafatawar ta baya bayan nan a birnin Ma’arib, ragowar 58 kuma ‘yan tawayen Houthi ne.

Mayakan na Houthi dai sun shafe makwanni sun kokarin kwace iko da birnin Ma’arib, wanda rasa shi zai zama babban koma baya ga gwamnatin Yemen dake samun goyon bayan dakarun kasar Saudiya dake jagorantar sauran sojojin kawance.

Yadda farmakin jiragen yaki ya ragargaza wani dakin taron masu halartar jana'iza a birnin Sana'a a kasar Yemen.
Yadda farmakin jiragen yaki ya ragargaza wani dakin taron masu halartar jana'iza a birnin Sana'a a kasar Yemen. AP - Hani Mohammed

A makon da ya gabata sama da mayaka 50 ne suka mutu daga bangaren sojin Yemen da na ‘yan tawayen Houthi yayin fadan da suka gwabza a birnin na Ma’arib.

A baya bayan nan dai, mayakan Houthi sun matsa wajen kokarin kaiwa wasu biranen Saudiya farmaki da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuki, said ai hakarsu ta gaza cimma ruwa, sakamakon kakkabo makaman da hukumomin tsaron kasar ta saudiya ke yi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.