Iran - Nukiliya

Iran ta gargadi Turai kan yi mata barazana gabanin tattaunawar Nukiliya

Shugaban Jamhuriyar Iran Hassan Rohani a Téhéran ranar 2 ga wata Dismabar 2020.
Shugaban Jamhuriyar Iran Hassan Rohani a Téhéran ranar 2 ga wata Dismabar 2020. AP

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya bukaci Turai da ta guji "barazana ko matsin lamba" kan duk wata tattaunawar da za a yi da Tehran, yayin da ya karbi bakuncin ministan harkokin wajen Ireland, a kokarin diflomasiyya na farfado da yarjejeniyar nukiliya mai muhimmanci.

Talla

Ireland a halin yanzu ta kasance mai shiga tsakanin Iran da wasu manyan kasashen duniya don mutunta ƙudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar ta 2015.

Yarjejeniyar, wacce aka fi sani da Joint Comprehensive Plan of Action a Turance (JCPOA), ta shiga rudani tun lokacin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya fice daga cikinta a shekarar 2018 kuma ya sake sanya takunkumi kan Tehran.

Bayan nasarar da Joe Biden ya samu a zaben shugaban kasar Amurka a watan Nuwamba, Amurka, kasashen Turai da suka kulla yarjejeniyar - Faransa, Jamus da Birtaniyya - da Tehran suna kokarin ceto yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.