Amurka-Coronavirus

Sabon shirin tallafawa Amurkawa ya tsallake rijiya da baya a majalisar dattijai

Harabar zauren majalisar dattijan Amurka.
Harabar zauren majalisar dattijan Amurka. AP - Alex Brandon

Shirin tallafawa Amurkawa da kuma farfado tattalin arzikin kasar daga radadin tasirin annobar Korona da ya kunshi dala tiriliyan 1 da biliyan 900 ya tsallake rijiya da baya a zauren majalisar dattijai.

Talla

‘Yan majalisar dattijan 50 ne suka kada kuri’ar amincewa da shirin tallafin na shugaba Joe Biden yayin da 49 suka hau kujerar naki.

A karkashin Shirin tallafin dai, za a rabawa gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi dala biliyan 350, dala biliyan 130 ga makarantu, sai kuma dala biliyan 49 da za a yi amfani da su wajen fadada Shirin yiwa mutane gwajin Korona, yayin da aka ware dala biliyan 14 don aikin raba alluran rigakafin cutar.

A halin yanzu daftarin Shirin zai sake komawa zauren majalisar wakilan Amurkan domin kada kuri’ar karshe na amincewa da shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.