Muhalli, Tarayyar Turai

Ayyukan masu sarrafa abinci na da alaka da gurbatar yanayi - Rahoto

Masu rajin kare muhalli na zafafa matsin lamba a kan gwamnatoci su kawar da fitar da hayaki mai gurbata muhalli.
Masu rajin kare muhalli na zafafa matsin lamba a kan gwamnatoci su kawar da fitar da hayaki mai gurbata muhalli. dpa/AFP/File

Wani rahoto da wata kungiya mai taken New Global research ta fitar ya bayyana cewa kaso daya bisa uku na gurbatar muhalli na da alaka da sarrafa abinci.Rahoton ya bayyana cewa, hayakin da ke fita ta kamfanonin da ke sarrafa abinci ne ke bada kaso daya bisa uku na gurbacewar muhalli.

Talla

Rahoton da kungiyar ta fitar  ya bayyana cewa sare bishiyoyi, zaizayar kasa, amfani da takin zamani ba bisa ka’ida ba, da kuma mu’amalantar dabobbi ta hanyar da bata da ce ba, na taka rawa wajen gurbata muhalli.

A cewar kungiyar, Irin gurbataccen bakin hayakin da kamfanonin sarrafa abinci ke fitar wa na zama barazana ga lafiyar jama’ar duniya sama da biliyan 7.

Kungiyar wadda ta ke hadin giwa da kungiyar tarayyar Turai, ta ce akwai bukatar gaggauta samar da wasu hanyoyin sarrafa abinci ta hanyar da ba zai zama ill aga lafiyar jama’a ba.

Baya ga sarrafa abincin akwai bukatar inganta yadda ake adana shi cikin mazubai, kasancewar su ma su na da ta su illar wajen gurbata muhallin.

 Sai dai rahoton ya ce wannan matsala na shafar kasa zuwa kasa la’akari da irin yawan kamfanonin sarrafa abincin da take da su.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.